PDP ta sauya wajen taro bayan ƴan sanda sun garƙame shalkwatarta

PDP PDP
PDP PDP

A yau Litinin ne jam’iyyar PDP ta sauya wurin gudanar da taron kwamitin amintattu na jam’iyyar daga dandalin Wadata Plaza, Sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja, zuwa cibiyar ‘Yar ’Adua da ke babban birnin tarayya Abuja.

Jam’iyyar ta yi zargin karbe iko da sakatariyar da wasu ‘yan sanda dauke da makamai daga rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja suka yi.

Wakilin gidan talabijin na Channels a Cibiyar ta Yar Adua, ya lura da isowar mambobin kwamitin amintattun tun da farko an hana su shiga filin na Wadata.

PDP ta bayyana mamayar jami’an yan sandan a matsayin musguna wa mambobin kungiyar ta hanyar hana su shiga sakatariyar don gudanar da taron nasu.

Rundunar ‘yan sandan ta hana mambobin kwamitin amintattun na jam’iyyar PDP da suka hada da Maina Chiroma da sauran jiga-jigai shiga harabar sakatariyar.

Wani tsohon sakataren jam’iyyar PDP na kasa Umar Tsauri, ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa ‘yan sanda sun dakatar da mambobin na kwamitin amintattun PDP, inda suka ce, sun yi hakan ne bisa umarni daga sama.

Mambobin kwamitin da ba su ji dadin lamarin ba daga baya sun fice daga sakatariyar yayin da ake ta takun-saka kan taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar NEC wanda shi ma aka shirya yi ranar Litinin.

A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta ce an tura ‘yan sanda zuwa sakatariyar jam’iyyar domin tabbatar da doka da oda.

A cikin wata sanarwa mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja Josephine Adeh ta fitar ta ce, “An tura jami’an ‘yan sanda zuwa wurin ne kawai domin tabbatar da doka da oda da kuma tabbatar da tsaron jama’a kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada, babu wani lokaci da ‘yan sanda suka rufe Sakatariyar.

Jam’iyyar PDP dai ta fada cikin rikicin cikin gida da aka kwashe shekaru ana fama da shi.

Rikicin ya haifar da dage taron na majalisar koli NEC na jam’iyyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here