Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya soki jagorancin Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa halin da Najeriya ke ciki a yanzu alama ce ta gazawa saboda cin hanci da rashin nagartaccen shugabanci.
Yayin da yake jawabi a taron Chinua Achebe Leadership Forum da aka gudanar a Jami’ar Yale, Obasanjo ya danganta matsalolin Najeriya da rashin kwarewa wajen shugabanci.
Da yake magana kan littafin Chinua Achebe na shekarar 1983 mai suna The Trouble with Nigeria, Obasanjo ya jaddada cewa babban matsalar kasar tana cikin gazawar shugabanni.
Har ila yau, ya ambaci ra’ayoyin masana kasa da kasa da ke bayyana Najeriya a matsayin kasa da ke fuskantar gazawa.
Obasanjo ya gargadi cewa cin hanci da kwace ikon kasa na haifar da illa ga hidimomin jama’a, ayyukan raya kasa, da kuma ci gaban tattalin arziki, yana mai kira da a dauki matakan gyara cikin gaggawa.
Jawabinsa ya sake tayar da muhawara kan kalubalen shugabanci da tsarin mulki a Najeriya.