Unguwar zoman UNICEF ta tsere daga hannun ISWAP bayan shekaru shida

UNICEFF Big

 

Wata unguwar zoma da ‘yan ta’addan ISWAP suka sace a shekarar 2018 ta samu ‘yanci bayan shafe shekaru shida a tsare.

Jami’ar lafiyan, Alice Loksha, an yi garkuwa da ita tare da wasu ma’aikatan lafiya mata biyu a ranar 1 ga Maris, 2018, yayin da suke aiki a cibiyar Hukumar Kula da Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) a Rann, karamar hukumar Kala Balge, Jihar Borno.

Da yake magana da ‘yan jarida a Maimalari Cantonment da ke Maiduguri a ranar Juma’a, Kenneth Chigbu, Mataimakin Kwamandan Rundunar Hadin Gwiwa ta (JTF) Operation Hadin Kai, ya bayyana cewa Loksha ta tsere daga tsarewar kuma an same ta a Geidam, Jihar Yobe, a ranar 24 ga Oktoba, 2024.

Chigbu ya bayyana cewa unguwar zoman mai shekaru 42 ta fuskanci aurar dole da wasu kwamandojin ISWAP biyu tare da tsananin wahala a tsare.

“Da farko an tsare ta a Tumbuma na tsawon kwanaki biyu kafin a mayar da ita Kwalleram, inda ta shafe watanni bakwai tare da auren wani shugaban ‘yan ta’adda mai suna Abu Umar.

“Wannan auren ya haifar da haihuwar dansu, Muhammad. Abu Umar ya rasa ransa yayin wani artabu da dakarun soji a shekarar 2022,” in ji Chigbu.

Bayan mutuwar Abu Umar, an sake tilasta wa Loksha auren wani kwamandan ISWAP mai suna Abu Simak a shekarar 2022.

Duk da haka, daga bisani abokan aikinsa sun kora shi zuwa sansanin Dogon Chukwu. Daga wannan sansanin ne Loksha ta samu damar tserewa ta Diffa har zuwa Geidam, inda ta kai rahoto ga dakarun JTF a ranar 29 ga Oktoba.

“Tuni aka yi mata gwaje-gwajen lafiya tare da ba ta tallafin jin kai,” in ji Chigbu.

Chigbu ya kuma tabbatar da tserewar Fayina Ali, kanwar marigayi Samuel Andrew, wani soja da ya yi aiki a ƙarƙashin Bataliya ta 212.

An yi garkuwa da Fayina ne a ranar 19 ga Oktoba, 2022, yayin da take kan hanyarta zuwa Maiduguri don kammala takardun fanshon dan uwanta.

“An tsare Fayina a Kangarwa na tsawon watanni tara kafin a mayar da ita Tumbuma na tsawon shekaru hudu. Daga bisani an dawo da ita Kangarwa, inda ta sake shafe wani shekara daya kafin ta tsere,” in ji shi.

An karɓi matan biyu a madadin gwamnatin Jihar Borno daga Zuwaira Gambo, kwamishinar harkokin mata da ci gaban al’umma ta jihar. Gambo ta tabbatar da cewa za a ba su tallafin kwantar da hankali da shirin farfadowa kafin a mayar da su ga iyalansu.

“Wannan mataki ne mai mahimmanci wajen farfadowarsu da sake shigarsu cikin al’umma,” in ji Gambo.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here