Ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore ta ƙasa, ta sanar da dakatar da shugabanninta na jihohin Taraba, Bauchi da Adamawa daga mukamansu nan take.
Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin Malam Mohammed-Suleiman, jami’in hulɗa da jama’a na ƙasa na ƙungiyar, a cikin wata sanarwa da aka fitar a Keffi, jihar Nasarawa a ranar Alhamis.
Mohammed-Suleiman ya bayyana cewa an yanke wannan hukunci ne bayan binciken korafe-korafen da aka samu daga wasu makiyaya na Fulani a waɗannan jihohi.
Ya ce Shugaban ƙasa na ƙungiyar, Alhaji Abdullahi Bodejo, ne ya yanke hukuncin dakatarwar bayan an tabbatar da sahihancin waɗannan koke-koke.
Ya ƙara da cewa shugabannin da abin ya shafa sun haɗa da Bammi Bello-Jane na Taraba, Muhammed Hussaini-Buzaye na Bauchi, da Usman Abubakar-Yirlabe na Adamawa, inda aka ce sun nuna rashin iya aiki da kuma sakaci wajen kula da walwalar membobin ƙungiyar.
Ƙungiyar ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin dawo da amincewar mambobi ga shugabancin ƙungiyar da kuma gyara tsarin shugabanci.
Haka kuma ta gargadi jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da kada su ci gaba da hulɗa da waɗannan shugabanni da aka dakatar, domin ba su da ikon wakiltar ƙungiyar.
Kungiyar ta kuma yi gargaɗin cewa duk wani yunkuri daga waɗanda aka dakatar na ci gaba da kiran kansu shugabanni zai haifar da gurfanar da su gaban kotu bisa doka. Ta ce ba za ta lamunci duk wani abu da zai bata sunanta ko kuma rage darajarta ba.
Shugaban ƙasa na ƙungiyar ya jaddada kudirinsa na kare muradun makiyaya Fulani a faɗin ƙasar nan tare da tabbatar da kyakkyawar walwala da ci gaban mambobin ƙungiyar.
NAN













































