Masu Garkuwa da Matata Sun Nemi Na Siyar da Motata Na Haɗa Masu Miliyan 8 – Basarake

BANDITS
BANDITS

Basaraken gargajiya na Bukpe da ke yankin ƙaramar hukumar Kwali a birnin tarayya Abuja, HRH Alhaji Hassan Shamdozhi, ya bayyana sakon da masu garkuwa suka aiko masa.

Basaraken, mai martaba a yankinsa ya ce ‘yan bindigan da suka yi garkuwa da matarsa sun aiko masa da sakon ya siyar da motarsa ta hawa ya haɗa musu miliyan N8m kuɗin fansa.

A ranar 4 ga watan Fabrairu, 2023, masu garkuwa suka kutsa gidan Sarkin suka yi awon gaba da ɗaya daga cikin matansa, Sadiya Hassan Shamdozhi tare da ‘ya’yansa maza 2.

Da yake zantawa da wakilin jaridar Daily Trust ta wayar tarho ranar Laraba, Basaraken ya ce ya shiga matsanancin yanayi game da batun garkuwa da matarsa da yaransa.

Ya ce masu garkuwan sun tuntube shi ranar Talata ta hannun ɗaya daga cikin ‘yan uwansa, sun umarci ya sayar da motarsa ta hawa domin ya harhaɗa kudin da suka nema fansa.

A kalamansa, Mai martaba Alhaji Hassan Shamdozhi ya ce: “Maganar gaskiya na shiga ruɗani, gobe Alhamis wata ɗaya kenan da sace matata da ‘ya’yana biyu.

“Lokacin da suka kira jiya Talata, sun faɗamun na siyar da motata na haɗa miliyan N8m kafin su sake su.”

“Da farko sun nemi miliyan N3m, ba zato suka sauya tunani suka koma miliyan N8m, sun ce ko motata na siyar na haɗa kuɗin.

“Ko da na sayar da motar ba zata wuce miliyan ɗaya ba.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here