Majalisar Wakilai ta bukaci INEC ta cire ‘yan takarar da ba sa cikin rajistar jam’iyyu

Reps Reps

Kwamitin Majalisar Wakilai mai kula da harkokin zaɓe ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta gudanar da bincike kan rajistar mambobin jam’iyyun siyasa, tare da hana ‘yan takarar zaɓen 2027 waɗanda sunayensu ba sa cikin rajistar mambobin jam’iyyunsu, kamar yadda Dokar Zaɓe ta 2026 ta tanada.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, shugaban kwamitin, Dan Majalisa Bayo Balogun na APC, ya ja hankalin INEC kan hukuncin Kotun Koli game da sassa na 77(5), 77(6) da 77(7), inda ya buƙaci a aiwatar da su gaba ɗaya ga dukkan jam’iyyun siyasa.

Ya ce shari’o’in da ke gaban kotu kan fassarar waɗannan sassa, da kuma batun ko sun yi daidai da kundin tsarin mulki da kuma yadda za a aiwatar da su, sun zo ƙarshe sakamakon hukuncin da Kotun Koli ta yanke.

Dan majalisar ya bayyana cewa a ranar 24 ga Satumba, Kotun Koli ta dawo da waɗannan tanade-tanade bayan ta soke hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara wanda ya bayyana su a matsayin waɗanda ba su dace da kundin tsarin mulki ba.

A cewarsa, Kotun Koli ta tabbatar da cewa waɗannan tanade-tanade ba su saɓa wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ba.

Balogun ya bayyana cewa Sashe na 77(5) ya tanadi cewa mambobin jam’iyya waɗanda sunayensu ke cikin rajistar mambobin da aka miƙa wa INEC kaɗai ne za su cancanci yin zaɓe ko a zaɓe su a zaɓen fidda gwani, tarukan majalisar jam’iyya da manyan tarukan jam’iyya.

Ya ce Sashe na 77(6) ya wajabta wa jam’iyyun siyasa su yi amfani da rajistar da suka miƙa wa hukumar zaɓe wajen gudanar da irin waɗannan ayyuka.

Balogun ya buƙaci INEC ta fara aiwatar da tanade-tanaden Sassa na 77(4) zuwa 77(6) ba tare da ƙarin jinkiri ba wajen gudanar da harkokin jam’iyyun siyasa da kuma sa ido kan ayyukan zaɓensu.

Dan majalisar ya ce binciken da INEC za ta gudanar ya kamata ya tabbatar da ko sunayen ‘yan takarar da jam’iyyun siyasa suka gabatar suna cikin rajistar mambobin da suka riga suka miƙa wa INEC bisa tanadin Sashe na 77(5).

“Wannan zai kasance wani babban gwaji ga hukumar duk jam’iyyar siyasa da ‘yan takarar da aka samu suna da laifi ya kamata a hana su shiga zaɓen.

“Tsauraran matakan aiwatar da wannan tanadi za su taimaka wajen hana rikice-rikice da kuma rage yawan shari’o’in da ka iya tasowa sakamakon zargin kura-kurai ko rashin bin tanade-tanaden Sassa na 77(4) zuwa 77(6) na Dokar Zaɓe.”

(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here