Babban Sakataren Majalisar Koli ta Shari’a a Najeriya (SCSN), Malam Nafiu Baba Ahmed, Esq., ya rasu.
Tsohon Minista kuma dan takarar gwamnan Gombe a jam’iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, ne ya sanar da rasuwarsa a ranar Talata a shafinsa na sada zumunta.
Read also: Hukumar EFCC ta kama wasu mutane 5 da ake zargi da yin damfara a Abuja
SolaceBase ta ruwaito cewa, bisa ga sakon, za a gudanar da sallar jana’izar marigayin a Masallacin Kasa, Abuja, jim kadan bayan idar da sallar Azahar a yau Talata.
Read also: Không Còn Mò Mẫm: Xu Hướng Chơi Casino Trực Tuyến Qua Lăng Kính Taixiumd5.link
Kodayake ba a bayyana musabbabin mutuwar ta sa ba.
“Cikin tsananin jimami, tare da cikakkiyar miƙa wuya ga hukuncin Allah, muna alhinin rasuwar Mallam Nafiu Baba Ahmed, Esq., wanda ya yi aiki a matsayin Sakataren na Majalisar Koli ta Shari’a a Najeriya (SCSN).”
Read also: Tsohon babban Lauya gwamnati Abubakar Malami ya tabbatar da amsa gayyatar hukumar EFCC
Sanarwar ta ce Nafiu Baba Ahmed ya sadaukar da shekaru 26 na karshen rayuwarsa wajen hidimtawa addinin Musulunci da dan adam, yana fafutukar tabbatar da adalci ga kowa.













































