Rundunar Sojin Sama ta Kasa (NAF) ta fitar da sunayen mutanen da suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin saman ATR 42 na rundunar da ya afku a yankin Igbokoda da ke Jihar Ondo ranar Litinin.
Jirgin, mai lambar NAF 931, na ɗauke da ma’aikatan biyar da fasinjoji 20, lokacin da ya yi hatsari yayin gudanar da aiki na yau da kullum daga Benin zuwa Legas.
Read also: HOTUNA: Ayyukan da Shugaba Buhari ya kaddamar a Kaduna
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar a ranar Talata, ya ce kawo yanzu ba a samu wani da ya tsira ba bayan hatsarin, lamarin da ya sa aka gaggauta fara aikin neman wadanda abin ya shafa tare da ceto su, inda aka hada gwiwa da hukumomin da abin ya shafa.
Mutanen da suka mutu sun hada da ma’aikatan jirgin guda biyar: Squadron Leader MI Aburime, matukin jirgin, Squadron Leader AP Man Ugwueje, mataimakin matukin jirgi, Flight Lieutenant IS Bako, mataimakin matukin jirgi, Warrant Officer Abubakar A, ma’aikacin gyaran jirgi da Corporal Uguru HC, ma’aikacin gyaran jirgi.
Fasinjoji 20 da suka mutu sun hada da Flight Lieutenant TL Lazarus, Flight Lieutenant M Akinloye, Flying Officer IM Adeshina, Master Warrant Officer Onwuka F, Master Warrant Officer Matini BA, Warrant Officer Nuhu FS, Flight Sergeant James RB, Flight Sergeant Mohammed AI, Sergeant Ani AE, Sergeant Izibenikien SI, Sergeant Alafuka C, Sergeant Mbadugha AN, Lance Corporal Ugwuba FC, Lance Corporal Eledan GE, Mrs Ezeh Nneka, Godstmine Tarabina, Joy Micheal, Sunday Micheal, Ukeme David da Gideon Omotola.
Read also: INEC ta ayyana zaben cike gurbi na jihar Zamfara a matsayin wanda bai kammala ba
Shugaban Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka mutu, ’yan uwa, abokai da sauran abokan aikinsu.
Aneke ya bayyana hatsarin a matsayin wani mummunan lamari mai matukar ɗaga hankali ga Rundunar Sojin Sama da kasa baki daya, inda ya tabbatar wa iyalan mamatan cewa rundunar za ta ba su cikakken goyon baya a wannan mawuyacin lokaci.
Ya kuma bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin.
A halin da ake ciki, hedikwatar Rundunar Sojin Sama ta Najeriya da ke Abuja ta bude kundin ta’aziyya, domin manyan jami’an gwamnati, jami’an diflomasiyya, shugabannin hukumomin tsaro da sauran masu fatan alheri su samu damar rubuta sakon ta’aziyya da girmama wadanda suka rasu tare da jajantawa iyalansu da Rundunar Sojin Sama.
Read also: DSS ta sake kama jagoran Ansaru wanda ya tsere a yayin harin da aka kai Gidan yarin Kuje
Daraktan Hulda da Jama’a da Bayar da Bayanai na Hedikwatar Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ne ya sanya hannu kan sanarwar.













































