Abokina ya samu rijiyar mai ba tare da amfani da dangantakar siyasa ba – Shettima

Kashim Shettima Gas

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa a yanzu ana bayar da rijiyoyin mai na Najeriya ne ta hanyar tsari na gaskiya da fafatawa tsakanin masu neman su, yana mai cewa wani abokinsa ya samu kadarar hakar man fetur ba tare da amfani da wata dangantakar siyasa ba.

Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a bikin cika shekaru biyar da kafa Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta Kasa (NUPRC), wanda aka gudanar a Abuja a ranar Talata, ya ce wannan ci gaban ya nuna irin gaskiya da sauye-sauyen da aka kawo a ɓangaren haƙar man fetur.

“A yanzu ana bayar da wuraren haƙar mai ne ta hanyar buɗaɗɗen tsari na gasa, kuma zan iya tabbatar da hakan. Wani abokina wanda ba shi da wata alaƙa ko kaɗan, ya samu wurin haƙar man fetur ta hanyar tsari na gaskiya da adalci.”

Ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta kuduri aniyar mayar da Najeriya ƙasar da masu zuba jari za su fi son zuwa domin zuba jari na dogon lokaci a harkar man fetur, yana mai tabbatar wa masu zuba jari cewa ƙa’idojin sun fito fili, kuma gwamnati za ta ci gaba da tabbatar da bin doka da ɗaukar alhaki.

Jawaban Mataimakin Shugaban Ƙasar sun zo ne a daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ke bayyana sauye-sauyen da ta ce ana aiwatarwa domin jawo sabon jari zuwa masana’antar mai da gas, ƙara yawan ɗanyen man da ake hakowa da kuma rage matsalolin da suka hana masu zuba jari bunƙasa albarkatun man fetur na ƙasar.

An kafa NUPRC ne bayan amincewa da Dokar Masana’antar Man Fetur ta 2021 (PIA), domin kula da ɓangaren haƙar man fetur da kuma sa ido kan yadda ake gudanar da albarkatun man ƙasar, ciki har da bayar da lasisi, yarjejeniyoyin hayar wuraren haƙar mai da kuma bunƙasa rijiyoyin mai.

Tun daga lokacin, hukumar ta gudanar da wasu matakai na bayar da lasisi da gasa, ciki har da zagayen neman lasisin haƙar mai na 2024 da 2025, wanda ya jawo hankalin kamfanonin cikin gida da na ƙasashen waje da suka nemi wuraren haƙar mai da aka tanada.

Shettima ya ce PIA ta kawo ƙarshen shekaru da dama na rashin tabbas a masana’antar, ta hanyar samar da ƙa’idoji masu kyau ga masu zuba jari, tare da bai wa al’ummomin da ake hako mai a yankunansu damar samun kaso mafi girma daga albarkatun da ke ƙarƙashin ƙasarsu.

“Shekaru biyar da suka gabata, PIA ta kawo ƙarshen shekaru ashirin na jira. Ina so in yaba wa Sanata Ahmed Lawan saboda rawar da ya taka wajen jagorantar amincewa da dokar PIA.

“Ta bai wa masu zuba jari ƙa’idoji bayyanannu, ta samar da tsarin da za a iya hasashe, sannan ta bai wa al’ummomin da ake hako mai a yankunansu, a karon farko, ikon mallakar albarkatun da ke ƙarƙashin ƙasarsu.”

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce an kafa NUPRC ne domin aiwatar da sabuwar dokar man fetur, yana mai cewa hukumar ta taimaka wajen inganta samar da man fetur da kuma dawo da amincewar masu zuba jari a ɓangaren haƙar man fetur na Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here