Kwalejin fasaha ta jihar Kogi da ke Lokoja ta gano wata tawaga da ke ƙirƙirar sakamakon jarrabawa na bogi, lamarin da ya kai ga dakatar da ma’aikata biyar, ciki har da mataimakin rajistara.
Shugaban kwalejin Farfesa Salisu Ogbo Usman, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da ya gudana a Lokoja, inda ya ce gano wannan abu babban barazana ne ga mutunci da amincin Kwalejin.
Ya bayyana cewa, bincike na musamman da sassan karɓar ɗalibai, fasahar sadarwa (ICT), da tsaro na jami’ar suka gudanar ne ya gano wata hanyar haɗin gwiwa da ta haɗa ɗalibai, tsoffin ɗalibai da wasu ma’aikata wajen ƙirƙirar sakamakon Diploma ta kasa (ND) da babbar Difloma ta ƙasa (HND) domin amfanin kansu.
Farfesa Ogbo ya ƙara da cewa duk da an dakatar da ma’aikata biyar daga aiki, wasu daga cikin waɗanda ake zargi, ciki har da wani mai suna Dominic Egwuda, har yanzu sun gudu.
Shugaban kwalejin ya kuma tabbatar da cewa, wannan lamari bai shafi tsarin tabbatar da inganci da tsaron jami’ar ba, domin hukumar tana da cikakken tsari na kare sahihancin takardun makaranta da amincin tsarin karatu.












































