Babbar kotun tarayya ta bayar da umarnin dakatarwa ga hukumar yiwa kamfanoni rajistar (CAC) da babban sakataren ta, da wasu hukumomi, da su tsaya a matakin da ake kan batun soke rijistar Majalisar Matasa ta Ƙasa (NYCN), bayan da shugaban ƙungiyar, Jakadan Sukubo Sara-Igbe Sukubo, ya kai ƙara kotu.
Rahotanni sun ce, an sake zaɓar Sukubo a matsayin shugaban majalisar matasan, duk da cewa ana ci gaba da samun shari’o’i kan rikicin shugabanci a cikinta.
Sai dai a ranar 7 ga Oktoba, ma’aikatar raya matasa ta sanar da cewa hukumar CAC ta soke rijistar majalisar, lamarin da ya jawo matakin daukar ƙara.
Kotun babbar birnin tarayya da ke Abuja ta bayar da wannan umarni a ranar 15 ga Oktoba, 2025, ƙarƙashin alƙaliya B. F. M. Nyako, inda ta ce, a tsaya matakin da ake kafin rikicin ya fara, tare da umartar a sanar da ɓangarorin da ke da hannu a shari’ar.
Ƙarar dai ta haɗa da Ƙungiyar Amintattu ta Majalisar Matasa ta Ƙasa da kuma Jakadan Sukubo Sara-Igbe Sukubo, wanda shi ne shugaban ƙungiyar kuma memba a hukumar amintattunta.
A ɓangaren da ake ƙara kuwa, sun haɗa da babban sakataren hukumar CAC, hukumar CAC kanta, ministan raya matasa na tarayya, da kuma ma’aikatar raya matasa ta tarayya.
Kotun ta sanya ranar 28 ga Oktoba, 2025, domin ci gaba da sauraron ƙarar, wadda ke neman hana waɗannan hukumomi soke rajistar majalisar, ko kuma aiwatar da wani mataki da zai iya shafar shugabancinta kafin an kammala sauraron shari’ar.
Wannan umarni na kotu na nufin cewa babu wani ɓangare da zai iya yin wani canji ga matsayin ƙungiyar har sai an yanke hukunci a gaba, domin tabbatar da adalci da zaman lafiya tsakanin ɓangarorin da ke rikicin.












































