Kotu ta daure wasu mutane 2 kan zargin yanke sassan jikin wata Mace

Kotu, daure, wasu, mutane, zargin, yanke, sassan, jikin, wata, Mace, Ibadan
Wata Kotun Majistare da ke Iyaganku da ke Ibadan, a ranar Talata, ta bayar da umarnin tsare wasu mutane biyu, Adekunle Fatai mai shekaru 40 da Sabitu Kolapo...

Wata Kotun Majistare da ke Iyaganku da ke Ibadan, a ranar Talata, ta bayar da umarnin tsare wasu mutane biyu, Adekunle Fatai mai shekaru 40 da Sabitu Kolapo mai shekaru 33, a gidan gyaran hali a Ibadan, bisa zargin yanke sashin jikin wata mata da kuma mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba.

An tuhumi mutanen biyu da ba a ba da adireshinsu ba da laifin hada baki da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

Alkalin kotun, Misis M. Olagbenro ba ta amsa rokon wanda ake kara ba saboda rashin hukunci.

Karin labari: Kotu ta kori karar da Iyalan Abacha suka shigar kan Gwamnatin Tarayya

Ta umarci ‘yan sanda da su mayar da fayil din karar zuwa ga daraktan kararrakin jama’a (DPP) domin samun shawarar lauya.

Daga nan ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 29 ga watan Oktoba, domin sake bibiyar shari’ar.

Dan sanda mai shigar da kara, Insp Elisha Tellang ya shaidawa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a ranar 13 ga watan Yuli da misalin karfe 11:35 na rana a kauyen Gbedun da ke Ibadan.

Karin labari: Jihohi 20 a Najeriya ciki harda Kano sun samu sabbin kwamandojin FRSC

Tellang ya ce wadanda ake tuhumar sun hada baki ne suka tono gawar wata mai suna Misis Oyindamola Olosunde tare da yanke mata kirjin ta na hagu.

Tellang ya ce wadanda ake tuhumar sun kuma mallaki bindiga ba tare da izini ba.

Ya ce laifukan sun ci karo da sashe na 6 (b) da na 3 na dokokin fashi da makami na Najeriya na shekarar 2004 da zama na 517 da 242(1) (b) na dokokin laifuka na jihar Oyo a 2000 kamar yadda NAN ta bayyana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here