Kisan Yelwata: Kotu ta tsare waɗanda ake zargi da ta’addanci

The nine suspected terrorists who attacked Yelwata in Benue on June 13 2026 at the Federal High Court in Abuja on Monday 750x430

Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare mutane tara a gidan gyaran hali na Kuje wadanda ake zargi da aikata ta’addanci, waɗanda ake tuhuma da kai hari cikin Al’ummar Yelwata da ke Jihar Benue, inda aka kashe kusan mutane 150, tare da tsare su.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta bayar da umarnin tsare su ne yayin zaman kotun na ranar Litinin, tare da dage sauraron shari’ar zuwa wasu kwanaki domin sauraron bukatar belinsu, bayan an gurfanar da su kan tuhume-tuhume 57 da suka shafi laifukan ta’addanci, inda suka musanta aikata laifukan da ake tuhumar su da su.

Bayan musun laifin da waɗanda ake tuhuma suka yi, Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya nemi kotu ta sanya ranar fara shari’a domin gabatar da shaidu, tare da roƙon kotu ta ba da umarnin tsare su a gidan gyaran hali har zuwa kammala shari’ar, la’akari da nauyin laifukan da ake tuhumar su da su.

Kotun ta kuma ƙi amincewa da buƙatar neman beli ta baki da lauyan wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma ya gabatar, inda mai shari’a ta umarce shi da ya shigar da buƙatar beli ta rubuce kamar yadda tsarin kotu ya tanada.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa NAN ya rawaito cewa ana zargin mutanen da kai harin ne a tsakanin wasu watanni a wata jiha makwabta kafin su kai farmaki Al’ummar Yelwata da ke Ƙaramar Hukumar Guma ta Jihar Benue, lamarin da ya haddasa kona gidaje da dama da kuma mutuwar kusan mutane 150 tare da jikkata wasu da dama.

Rahoton ya ƙara da cewa jami’an tsaro daban-daban ciki har da Hukumar Tsaro ta DSS ne suka haɗa kai wajen cafke waɗanda ake zargin, kafin a gurfanar da su a gaban kotu kan zargin shirya kai hare-haren ta’addanci da kuma aiwatar da su.

An bayyana sunayen mutanen tara da aka gurfanar da su, yayin da kotu ta amince da cire sunan wani mutum guda daga cikin jerin waɗanda aka fara shigar da ƙara a kansu, bayan roƙon da Babban Lauyan Ƙasa ya gabatar, lamarin da ya samu amincewar lauyoyin ɓangaren kariya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here