Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta kama mutane tara bisa zargin hannu a harin da taron jama’a suka kai ofishin ‘yan sanda na Garko, bayan kama wasu mutane uku da ake zargi da kisan kai.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Kiyawa ne ya bayyana hakan, yana mai cewa lamarin ya faru ne ranar 5 ga Satumba 2025 lokacin da aka kawo wadanda ake zargin zuwa ofishin don bincike.
Sai dai, wasu tawagar jama’a dauke da duwatsu da sanda suka kai hari kan ofishin, suna zanga-zangar kisan da aka yi tare da yunƙurin kashe wadanda ake tsare da su.
Wannan farmaki ya haddasa kona motar sintiri ta ‘yan sanda da lalata motoci uku na Hisbah da na Karamar Hukumar Garko, tare da fashe gilasan ofishin.
Labari mai alaƙa: Kano: ‘Yan sanda sun kama sama da mutane 100 da ake zargi da aikata laifuka cikin sabon shirin “Operation Kukan Kura”
A yayin rikicin, jami’ai uku sun jikkata kuma an garzaya da su asibitin Wudil, inda ake musu magani. Haka kuma, wani mutum daga cikin masu farmakin ya rasu bayan wata tayar da ke ci tana ƙonewa ta fashe ta bugi jikinsa, yayin da wasu uku suka jikkata.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya tura jami’ai don kwantar da tarzoma tare da haɗa kai da shugabannin al’umma domin dawo da zaman lafiya. Ya kuma tabbatar da cewa an kama mutane tara, yayin da bincike ke ci gaba domin gano sauran masu hannu a ciki.
Bakori ya ja hankalin jama’a da su guji daukar doka a hannunsu, yana mai cewa irin wannan hali na kawo rudani da rashin zaman lafiya. Ya jaddada cewa jama’a su rika kai koke da korafe-korafensu ga hukumomin da suka dace maimakon tashin hankali.
Kwamishinan ya sake tabbatar da jajircewar rundunar wajen kare rayuka da dukiyoyi tare da tabbatar da adalci. Ya kuma tunatar da jama’a kan matakin da ‘yan sanda suka dauka tun a watan Yuni 2025 wajen yaki da ta’addanci da ayyukan ‘yan daba a Kano, inda ya yi gargadin cewa ba za a lamunci ayyukan tada rikici ba.











































