Jami’ar Jos ta tabbatar da kishe wani ɗalibi da abokinsa ya yi

UNIJOS 750x418

Hukumar gudanarwar jami’ar Jos ta tabbatar da kisan ɗalibinta mai suna Peter Mafuyai, ɗalibi a mataki na uku a sashen kasuwanci da kuɗi, wanda abokinsa kuma ɗalibin jami’ar ya kashe.

Hukumar gudanarwa ta jami’ar Jos ta tabbatar da mutuwar ɗalibinta mai suna Peter Mafuyai, ɗalibi a mataki na uku a sashen kasuwanci da kuɗi, wanda abokinsa ɗalibi a jami’ar ya kashe.

Rajistar jami’ar, Dakta Rejoice Songden, ce ta tabbatar da lamarin a cikin wani saƙon ta’aziyya da ta fitar ranar Litinin a Jos.

Ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a wajen harabar jami’ar, ba a cikin makaranta ba, kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai suka ruwaito ba daidai ba.

Ta ƙara da cewa marigayin ɗalibin an kashe shi ne da ake zargin abokinsa Nanpon Timnan, ɗalibi a shekara ta biyu a sashen kimiyyar gona.

Hukumar gudanarwa ta jami’ar ta miƙa ta’aziyya ga iyalan mamacin, abokansa da sauran ɗalibai, tare da fatan Allah Ya ba su haƙuri da juriya.

Ta kuma bayyana cewa shekarar karatu ta 2024/2025 ta ƙare tun ranar 30 ga watan Agusta, kuma ana sa ran ɗalibai za su koma makaranta ranar 10 ga watan Nuwamba don sabon zangon karatu na 2025/2026.

Songden ta tabbatar da cewa jami’ar na aiki tare da hukumomin tsaro domin gudanar da cikakken bincike da tabbatar da adalci kan lamarin.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here