Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka (ICPC) ta samu nasarar gurfanar da shugaban rikon ƙwarya na ƙaramar hukumar Sakaba a Jihar Kebbi, Abubakar Bawa Makuku, da kuma daraktan kuɗi da kayan aiki na hukumar, Ahmed Abdullahi Fakai, bisa laifin yin amfani da kujerunsu wajen aikata zamba ta Naira miliyan 54.
Rahoton Solacebase ya bayyana cewa an gurfanar da su a gaban mai shari’a E. Gakko na babbar kotun tarayya da ke Birnin Kebbi bisa tuhume-tuhume da suka shafi cin hanci, bayar da kwangiloli ba bisa ƙa’ida ba, da kuma yin amfani da kuɗaɗen gwamnati ba bisa doka ba.
A lokacin shari’ar, lauyan gwamnati, Hamza Sani, ya gabatar da hujjoji da suka tabbatar cewa Fakai ya cire jimillar kuɗin Naira miliyan 54 daga asusun ƙaramar hukumar Sakaba a lokuta guda shida, domin gujewa bin ƙa’idojin bayar da rahoton kuɗi.
A wata sanarwa da daraktan wayar da kai da ilimantarwa na ICPC, Mista Demola Bakare, ya fitar a ranar Juma’a, an bayyana cewa kotu ta kuma tabbatar da cewa Makuku ya bayar da kwangiloli ba tare da bin tsarin gwamnati ba, tare da karkatar da Naira miliyan 10 da aka ware don ayyukan hukuma zuwa amfanin kansa.
Alƙalin kotun, bayan sauraron shari’ar, ya same su da laifi bisa hujjojin da aka gabatar, inda ya yanke wa Fakai hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan yari ko biyan tara ta Naira miliyan 2.5, yayin da Makuku ya samu hukuncin ɗaurin shekaru huɗu ko biyan tara na Naira miliyan 2.5, ciki har da Naira miliyan 1 da zai biya a matsayin diyya ga ƙaramar hukumar Sakaba.
Wannan hukunci, a cewar hukumar ICPC, na nuni da ƙudirin hukuma na tabbatar da cewa duk wani jami’in gwamnati da ya ci amanar ofishinsa ko ya karkatar da dukiyar jama’a, zai fuskanci hukunci bisa tanadin doka.













































