Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta lalata sama da kilogiram 560 na maganin da ta kama daga masu safarar miyagun kwayoyi a Jihar Legas.
Shugaban hukumar Birgediya Janar Buba Marwa Mai ritaya wanda shi ne ya sa ido yayin Kona kwayoyin ya gargadi masu safarar miyagun kwayoyi kan su guji aikata hakan.
Marwa ya ce, rundunar ‘yan sandan yankin Seme da kuma hukumar NDLEA reshen jihar Legas ne suka kama wadannan kwayoyi, inda ya kara da cewa wasu ma sun fito ne daga cibiyar adana kayayyakin hukumar.
Ya ce an kama wasu magungunan ne tsakanin shekarar 2019 zuwa watan Yulin 2022.
Daga cikin magungunan da aka lalata akwai tabar wiwi da hodar iblis da tabar heroin da methamphetamine.
Sauran sun hada da Tramadol da Ephedrine da Codeine na ruwa dana da na kati da sauran kwayoyi.
Marwa ya ce wannan kayan shi ne mafi girma da aka kone tun kafuwar hukumar ta NDLEA, inda ya bukaci masu Sha da fataucin magunguna da su nemi wasu ayyukan yi.
Ya kuma nuna jin dadinsa da kamun wanda ya danganta shi da kwazon da jami’an hukumar suka yi.

Mista Abubakar Wada, kwamandan sashin hukumar NDLEA, reshen Seme, ya yabawa ’yan uwansa jami’ai bisa yadda suke ba da gudunmuwar da suke yi wajen kama miyagun kwayoyi.













































