edikwatar tsaro ta (DHQ) ta yi magana kan batun naɗa muƙaddashin hafsan sojojin Najeriya (COAS). DHQ ta sanar da cewa ba ta naɗa wanda zai zama COAS yayin da Taoreed Lagbaja ya tafi hutu ba.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da muƙaddashin daraktan yaɗa labarai na tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya fitar a ranar Litinin a shafin X na DHQ.
Tukur Gusau ya ce babu irin wannan naɗin a cikin rundunar sojojin Najeriya, yana mai cewa babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya yi magana da Taoreed Lagbaja ƴan mintuna kaɗan da suka gabata. A cewarsa, hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, a halin yanzu ya tafi hutu ne. Ya bayyana cewa ana tafiyar da rundunonin sojoji cikin ƙwarewa, ya ƙara da cewa dukkanin hafsoshin tsaro na gudanar da ayyukansu kamar yadda kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya tanada.
Birgediya Janar Tukur Gusau ya fayyace cewa Manjo Janar Abdulsalam Ibrahim, wanda shi ne shugaban sashen tsare-tsare, ya na ba da bayanai ga Lagbaja kan ayyukan rundunar na yau da kullum.