Gwamnatin Kano Ta Sake Bude Cibiyoyin Bada Horon Sana’o’i 26 Da Ganduje Ya Rufe.

Abba Kabir Yusuf.jpeg

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da bude cibiyoyin bada horon sana’o’i guda 26 da gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ta rufe abaya.

Kwamishinan ayyuka da gidaje Marwan Ahmad ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Kano.

“Gwamna Abba Kabir-Yusuf ya bayar da umarnin a bude dukkanin cibiyoyin kasuwanci guda 26 da gwamnatin Sen. Kwankwaso ta kafa wadanda gwamnatin da ta shude ta yi watsi da su,” in ji Mista Ahmad.

Ya ce gwamnatin Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso ta kafa cibiyoyin ne domin baiwa matasa da mata sana’o’i daban-daban.

Za a yi amfani da cibiyoyi yadda ya kamata wajen magance shaye-shayen miyagun kwayoyi da ‘yan daba, lamarin da ke matukar cin ran kanawa.

“Cibiyoyin sun hada da aikin jarida, aikin gona, kiwon kaji, tuki, da yawon buɗe ido, kiwon dabbobi, wasanni, ilimin bayanai, da Tsaro na kamfanoni, da sauransu,” in ji shi.

A cewarsa, za a yi amfani da cibiyoyin da suka fi dacewa wajen magance shaye-shayen miyagun kwayoyi da ‘yan daba, lamarin da ke da matukar damuwa ga mazauna jihar.

Ya ce gwamnan ya kuma umarci ’yan kwangilar da ke tafiyar da ayyukan tituna mai tsawon kilomita 5 da gwamnatin Kwankwaso ta fara a fadin kananan hukumomin jihar 44 da su koma bakin aiki a wuraren.

Mista Ahmad ya ci gaba da cewa, haka ma gwamnatin jihar ta koma bakin aiki a aikin titin wuju wuju dake Jakara da aka yi watsi da shi a cikin birnin Kano.

Kwamishinan ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na samar da ababen more rayuwa domin inganta rayuwar jama’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here