Kwamitin ganin wata a kasar Saudiyya ya bayyana cewa ba’a ga jinjirin watan Shawwal a kasar Saudiyya a yau Talata ba.
Sakamakon haka, watan Ramadan mai alfarma zai ci gaba har zuwa ranar 9 ga watan Afrilu, wanda zai dauki kwanaki 30.
Don haka za’a yi Eid Al Fitr ne a ranar 10 ga watan na Afrilun 2024.
Karin labari: ‘Yan ta’adda sun kashe masu aikin sa kai na tsaro su 30 a jihar Neja
Kotun kolin kasar Saudiyya ta yi kira ga daukacin al’ummar musulmin kasar da su duba jinjirin watan Shawwal a yammacin ranar Litinin 29 ga watan Ramadan.
Ganin jinjirin watan Shawwal shi ne karshen watan Ramadan mai alfarma da kuma farkon watan Idi.
Karin labari: Kotu ta ci gaba da tsare Emefiele kan zargin almundahana da zamba
Tun da farko dai cibiyar nazarin taurari ta duniya ta bayyana cewa, wasu kasashen da suka nuna jinjirin watan Ramadan a ranar Litinin 11 ga watan Maris, za su sa ran ganin jinjirin watan a ranar Litinin 8 ga watan Afrilu.
To sai dai ba’a san ganin watan ba saboda faduwar wata kafin rana. yana haifar da haɗuwa da ke faruwa bayan faduwar rana.