Gwamnatin tarayya ta tanadi karin kudi na musamman na N470bn a kasafin kudin 2023 don karin albashin malaman jami’o’in Najeriya da kudin gyara jami’o’in.
Ministar kudi, Zainab Ahmed, ta bayyana hakan ranar Laraba yayin hira da manema labarai a fadar shugaban kasa, rahoton ChannelsTV.
Ta ce musamman aka yi wannan karin don Malaman jami’an da suka kammala yajin aiki makon da ya gabata. Tace za’a yi karin albashi da N170bn sannan a gyara jami’o’in da N300bn.
A cewarta, har yanzu gwamnati ta shan wahalar samun kudin shiga.
Game da wasu rassa kuwa, tace an tanadi 2.05 trillion don sashen Ilimi yayinda aka tanadi 1.58tr don kiwon lafiya. Hakazalika aka ware 2.74tr don tsaro sannan aka tanadi 998.9 billion don manyan gine-gine, sannan 756 billion don rage talauci.













































