Gwamna Yusuf ya taya Kwankwaso murnar cika shekaru 70, ya yaba da gudummawarsa ga ci gaban Kano

R L Rabiu Musa Kwankwaso and Abba Kabir Yusuf 640x430

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya taya tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, murnar cika shekaru 70 da haihuwa.

Gwamna Yusuf ya bayyana wannan rana a matsayin wata muhimmiyar dama ta bikin rayuwar Sanata Kwankwaso, jagorancinsa da gudummawar da ya bayar wajen ci gaban Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.

Hakan na ƙunshe ne cikin saƙon taya murnar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Talata.

Gwamnan ya amince da irin rawar da Kwankwaso ya taka wajen bunƙasa harkokin siyasa a jihar.

Ya ce zagayowar ranar haihuwar tsohon gwamnan wata dama ce ta yin nazari kan shekarun da ya shafe yana hidimar jama’a, da kuma gudummawar da ya bayar a fannin shugabanci, bunƙasa ababen more rayuwa da faɗaɗa damar shiga harkokin dimokuraɗiyya a Jihar Kano.

Gwamna Yusuf ya yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba tsohon Ministan Tsaro, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ƙoshin lafiya, tsawon rai da sabon ƙwarin gwiwa domin ci gaba da bayar da gudummawa ga ci gaban jihar da ƙasa baki ɗaya.

Haka kuma, ya yi masa fatan ƙarin shekaru masu cike da zaman lafiya da farin ciki yayin da yake bikin wannan gagarumar nasara ta cika shekaru 70 da haihuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here