Mukaddashin gwamnan jihar Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, ya Yana da kwazon kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, bisa doke DMD FC ta Maiduguri da ci 2-0 a gasar cin kofin Aiteo zagaye na 16 da aka buga ranar asabar a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi.
Ta cikin wata sanarwa da Gawuna, ya fitar dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran sa Hassan Musa Fagge, ya danganta nasarar da kungiyar ta SAI MASU GIDA’’ ta samu a matakin dab da na kusa da na karshe na gasar, a matsayin nuna himma da kwazon Kungiyar.
“Gwamnatin jihar nan a karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da mutanen Kano gaba daya suna alfahari da ku sakamakon sanya farin ciki a zukatansu”.
“Yayin da kuke shirin tunkarar wasan ku na gaba ranar Laraba, muna son ku lashe sauran wasannin ku sake maimaita irin nasarorin da kuka samu shekaru uku da suka gabata ta hanyar lashe kofi mai daraja a jihar Kano”.
“Muna kuma jinjina wa jama’ar jihar da magoya bayan Kungiyar, bisa ci gaba da goyon baya da addu’o’i ga tawagar”.
“Ina kuma tabbatar da gwamnati za ta ci gaba da bada gudunmawarta ga kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da kuma jajircewa wajen saka hannun jari a harkokin wasanni.” A cewar Gawuna.