EFCC ta kuduri aniyar ƙarfafa haɗin gwiwa da ‘yan jarida a Kano wajen yaƙi da cin hanci

WhatsApp Image 2025 09 30 at 14.52.57 750x430

Hukumar yaƙi da cin Hanci da rashawa (EFCC) ta bayyana shirinta na ƙara zurfafa alaƙar haɗin gwiwa da ƙungiyar ƴan Jarida masu bayar da rahotanni a Kano (Correspondents’ Chapel) don tabbatar da nasara a yaƙin da ake yi da rashawa da sauran laifukan kuɗi.

Shugaban hukumar a Kano, Sa’ad Hanafi Sa’ad, ne ya bayyana haka a lokacin da ya karɓi shugabannin ƙungiyar a ofishinsa ranar Talata.

Ya ce, kafafen yaɗa labarai su ne ginshiƙai a yaƙin da ake yi da cin hanci, saboda suna bayar da haske, da fallasa laifuka da kuma tabbatar da gaskiya ga al’umma.

Sa’ad ya jaddada cewa ƙofofin hukumar a bude suke ga haɗin gwiwa da ‘yan jarida, yana mai kira gare su da su tabbatar da sahihancin labarai kafin wallafawa, tare da bin tanade-tanaden dokar kafa EFCC ta 2004 da ta bai wa jama’a damar kai rahoto kan laifukan kuɗi ko da ba tare da rubutaccen ƙorafi ba.

Ya ce EFCC ba wai kawai bincike da gurfanarwa take yi ba, har da wayar da kan jama’a kan illolin cin hanci ga ci gaban ƙasa.

Karanta: ICPC ta gurfanar da mutane biyu a kotu kan damfara da jabun takardar aiki na Naira miliyan 4.8

Haka kuma ya nuna shirinsu na tallafa wa wajen bada horo da bita ga ‘yan jarida don ƙara ƙwarewa a rahoton yaƙi da cin hanci.

Da yake jawabi, shugaban ƙungiyar, Murtala Adewale, ya yi kira da a samar da kyakkyawar alaƙa tsakanin EFCC da ‘yan jarida domin al’umma su ci gajiyar hakan.

Ya kuma sanar da hukumar shirinsu na yin taron bita na ƙungiyar mai taken “Solution Journalism”, yana mai neman goyon bayan EFCC.

Adewale ya yaba wa hukumar bisa ƙoƙarin da take yi wajen yaƙi da laifukan kuɗi duk da ƙalubalen da ake fuskanta, yana mai cewa haɗin gwiwa da kafafen yaɗa labarai zai ƙara ƙarfafa wannan yaƙi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here