Hukumar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana cewa ta kama mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam, Omoyele Sowore, ne saboda jagorantar masu zanga-zanga zuwa wurin da kotu, bayan ta hana yin zanga-zanga a Abuja.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na ƙasa, CSP Benjamin Hundeyin, ne ya bayyana haka a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.
Ya ce an kama Sowore ne bayan wasu mutum 13 da aka cafke a baya yayin zanga-zangar “Free Nnamdi Kanu” suka bayyana cewa shi ne ya jagorance su zuwa yankin da kotu ta hana shiga.
Hundeyin ya ce ba zai zama adalci a gurfanar da waɗanda aka kama ba tare da kama wanda ya jagorance su zuwa wurin da aka hana ba.
Labari mai alaƙa: Ƴan sanda sun kama Sowore a kotun Abuja
Saboda haka, don tabbatar da daidaito da bin doka, jami’an tsaro suka kama Sowore domin ya amsa tambayoyi.
Ya ƙara da cewa Sowore ba zai shafe fiye da awa 24 a hannun ‘yan sanda ba, domin ana shirin gurfanar da shi a gaban kotu da zarar an kammala rubuta tuhume-tuhumensa.
A cewarsa, mutum 13 da aka kama a baya sun keta umarnin kotu da ta hana gudanar da zanga-zanga a wasu sassan Abuja, ciki har da yankin Transcorp da ma’aikatar kuɗi, inda aka kama su kuma aka gurfanar da su cikin sa’o’i 24.
NAN













































