Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da takwaransa na jihar Bauchi, Bala Mohammed, da kuma Dauda Lawal na jihar Zamfara suna gaban kotu domin shaida yadda shari’ar za ta gudana a kotun koli.
Haka kuma shugaban jam’iyyar PDP na kasa Umar Damagum da gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, suma suna cikin kotun.
Karanta wannan: Gwamnatin tarayya ta sake yin alkawarin kammala titin Abuja zuwa Kaduna a wannan Shekara
Ana sa ran kotun kolin za ta yanke hukunci kan kararrakin da aka yi na gwamnoni bakwai.
Jihohin sune Legas da Kano da Zamfara da Plateau da Ebonyi sai Bauchi da kuma Cross River.



