Babban bankin kasa (CBN) ya yi watsi da wani rahoto da ya yi ikirarin cewa ya gabatar da takardar kudi Naira 5,000 da kuma Naira 10,000 domin saukaka hada-hadar kudi a matsayin labarin karya.
A wata sanarwa da babban bankin ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana rahoton a matsayin na bogi, ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da shi.
Sanarwar da sashen sadarwa na CBN ya fitar ta ce, “Bayanan abin ba daga babban bankin Najeriya ba ne.
Rahoton na bogi ya ruwaito cewa, daya daga cikin mataimakin gwamnan babban bankin kasa CBN, Ibrahim Tahir Jr., ya dauki wannan mataki ne da nufin rage kashe kudaden da ake kashewa wajen tafiyar da harkokin kudi da kuma samarwa ‘yan Najeriya hanyoyin da suka dace na gudanar da manyan hada-hadar kasuwanci.
Har ma a ciki aka bayyana cewa sabuwar takardar Naira 5,000 za ta kunshi hoton Cif Obafemi Awolowo, yayin da takardar Naira dubu 10,000 za ta dauki hotob Dakta Nnamdi Azikiwe, domin nuna irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban Najeriya.
Rahoton na karya ya kuma ce za a fara fitar da sabbin takardun kudi a fadin kasar a ranar 1 ga Mayu 2025, inda aka umarci bankunan kasuwanci da su fara fitar da sabbin takardun kudi ta hanyar ATMs da kuma hada-hadar saye da sayarwa.