An aika wa Sanata Natasha wasiƙar da ƴan mazaɓarta suka tura na neman yi mata kiranye

9c285566 9622 4334 83a0 d85be7d7912f.jpg

Hukumar zaɓe ta kasa INEC, ta aike wa Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan sanarwa a hukumance kan koken da ƴan mazaɓarta suka kai na ƙoƙarin yi mata kiranye daga majalisa.

INEC ta kuma tabbatar da samun cikakkun lambobi da adireshin wakilan da suka tura koken da takardun sanya hannu kan batun yi mata kiranyen.

Wakilan sun aika bayanan nasu masu muhimmanci ne cikin wata wasiƙa ga shugaban hukumar.

A cewar ƴan mazaɓarta, suna ƙoƙarin yi wa sanatan kiranye ne saboda ba ta wakiltar su yadda ya kamata.

Karin karatu: Majalisar wakilai ta janye amincewa da ƙudurin cire rigar kariya ga mataimakin shugaban kasa da gwamnoni bayan karatu na biyu

A baya INEC ta bayyana cewa a shirye ta ke ta bi matakan da kundin tsarin mulki ya shimfiɗa mata na yin irin wannan kiranye da zarar masu ƙorafin sun cika ƙa’idojin da doka ta gindaya.

Sanata Natasha dai na fuskantar kiranye ne tun bayan taƙaddamar da ta ɓarke tsakaninta da shugaban majalisar dattijan Najeriya Godswill Akpabio bayan ta zarge shi da yunƙurin cin zarafi na lalata.

Aika, An aika wa Sanata Natasha wasiƙar da ƴan mazaɓarta suka tura na neman yi mata kiranye.

BBC

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here