Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya ta ce jami’anta sun kashe wasu mutum biyu da ake zargi da garkuwa da mutane a garin Rafin Gora da ke ƙaramar hukumar Ningi a jihar, tare da kuɓutar da wani mutum guda da ake zargi sun yi garkuwa da shi.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Ahmed Wakil ya fitar ranar Lahadi, ya ce mutanen ɗauke da makamai sun kai hari wani gida a garin Rafin Gora tare da yuƙurin sace wani mutum mai shekara 28.
Sanarwar ta ce ”mutumin ya nuna turjiya ga masu garkuwar, lamarin ya janyo suka harbe shi a loƙacin da yake ƙoƙarin guduwa”.
“Daga nan ne ‘yan sanda tare da haɗin gwiwwar ‘yan sa-kai suka kai ɗauki wurin da lamarin ke faruwa, inda suka yi musayar wuta da su, inda mutum biyu daga cikin maharan suka gamu da ajalinsu, tare da ƙwace bindiga ɗaya ƙirar AK47”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
SP Wakil ya ce ‘yan sanda sun kuɓutar da mutumin da masu garkuwar suka yi yunƙurin sacewa, inda nan take aka garzaya da shi babban asibitin tarayya da ke Birnin Kudu domin yi masa magani.
Ya ƙara da cewa rundunar ‘yan sanda ta ƙaddamar da farautar mutanen domin su fuskanci hukunci.













































