Hukumar shige-da-fice ta kasa (NIS) ta kore jami’anta 4, tare da ragewa 14 mukami bisa kamasu da laifin rashin da’a a gurin aiki.
Mai magana da yawun hukumar ne, DCI Tony Akuneme, ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar talata a abuja.
Sanarwar tace an kore jami’an ne bayan an gorafanar dasu a gaban kwamatin ladafftarwa na hukumar.
Sanarwar ta kara dacewa yanke hunkuncin na da alaka da yunkurin gwamnatin tarayya na yaki da cin hancin da rashawa.
“Mun chanjawa Jami’ai biyu wurin aiki, yayin da 11 muka tura musu da wasikar kashedi, haka kuma mutum daya daga cikin jami’an namu muka tillastawa masa yin ritayar dole.” inji sanarwar
“Yanzu haka akwai mutum 11 da suke jirarn shara’a a gaban kwamatin laddafatrwa domin sanin makomar su, sanan kuma mutum hudu sun rasa aikin su a halin yanzu.”
sanarwar ta kuma kara da jan hankalin jama’a dasu kula sosai domin taimakawa hukumar domin gudanar da aikinta yacce ya dace.
“Ga duk wanda keda wani kurafe zai iya tura mana sako kartakwana ta wadanan hanyoyin +2348033074681; +2348021819988; (b) Twitter: @nigimmigration and email: is.pro@immigration.gov.ng”.













































