Duk da yunƙurin da ƴan gaza gani keyi na disashe irin nasarorin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta samu, tarihi zaiyi matukar kyawu tareda yin adalci gare shi.
Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a wajen bikin kaddamar da jerin kundi da Shugaban kasa ya samar (2015-2023) wanda ma’aikatar ta shirya.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya rawaito rahoton cewa, kundin ya kunshi aikace aikacen ministan ayyuka da gidaje, Mista Babatude Fashola.
A jawabinsa na bude taron, Mohammed ya bayyana cewa, masu fafutuka dakile nasarorin Buhari na kokarin dakushe dimbin nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu, yayin da suke siyasantar da al’amuran.
Ya jaddada cewa gwamnati ta aiwatar da ayyuka masu tasiri a fadin kasar nan wadanda suka cika burin ’yan Najeriya kuma tarihi zai yi wa gwamnatin adalci.
“Yaran ‘yan makaranta samada miliyan 9 da ake ciyar da su a kullum; Matasa miliyan 1 da aka ba wa aikin yi, da kuma matasa dubu 500 da ke samun horo a karkashin shirin N-Power ba za su manta da wannan gwamnati ba.
“Magidanta Milyan 1,632,480 da aka yiwa rajista a cikin tsarin da ake turawa kudade su ma ba za su manta da shirye-shiryen jin daɗin da gwamnatin ta samar ba,” in ji Mohammed.
Ministan ya ce an tsara irin dimbin nasarorin da gwamnatin ta samu yayin da ta ke kara tabbatar da managartan ayyuka kafin cikar waadinta.
Ya kuma ba da tabbacin cewa ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati za su fito a cikin jerin shirye-shiryen don baje kolin irin nasarorin da suka samu a ma’aikatu da sassansu daban-daban.
A zaman na ranar Laraba ya samu halartar karamin minista a ma’aikatar ayyuka da gidaje, Alhaji Umar El-Yakub da ministan babban birnin tarayya, Alhaji Mohammed Bello.
Har ila yau, a wajen taron akwai karamin ministan kimiyya da fasaha, Mista Ikechukwu Ikoh da manyan jami’an gwamnati a ma’aikatar yada labarai da al’adu.












































