Ba Abu Ne Mai Yiwuwa Ba Mu Sa Jami’ai Su Tsare Kowane Sashe Na Kan Iyakar Najeriya -Aregbesola

013b0000 0aff 0242 709b 08daab21499d w1597 n r1 st s
013b0000 0aff 0242 709b 08daab21499d w1597 n r1 st s

Ministan Cikin Gida na Najeriya Ra’uf Aregbesola ya ce Najeriya za ta rungumi hanyoyin kimiyya na tauraron dan-adam wajen kula da kan iyakokin kasa da tsawon su ya kai kilomita 5000.

Aregbesola wanda ke amsa tamboyin manema labaru, ya ce ba zai yiwu a tura jami’ai ko ina su rika kula da tsaron kan iyakokin ba. Ya ce Najeriya na daga kasashe uku mafiya fadin kasa a Afirka, don haka ba zai yiwu a ce kowane inci na kan iyakarta za a iya girke jami’an tsaro don kula da shi ba. Wannan dalili, inji Aregbesola, ya sa kasar ta ke gab da rattaba hannu kan wata yarjejeniya da wani kamfanin kasar Sin don samar da na’urorin tauraron dan-adam da za su rika zuba ido kan iyakokin dare da rana.

Ministan ya kara da cewa akwai wani kalubale da ya shafi kan iyakokin na raba jama’a masu al’ada iri daya ya zama wannan gefe ya na wannan kasa wannan gefe kuma ya na waccar kasar.

(VOA)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here