Ambaliyar tiga: Dan Majalisa ya bukaci Gwamnatoci dasu tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Kano

IMG 20220911 WA0195
IMG 20220911 WA0195

Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Rano-Kibiya-Bunkure Kabiru Alhassan Rurum ya roki gwamnatin tarayya da ta jihar Kano da su gaggauta kai dauki ga dubban al’ummar da ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a Tiga Dake barazana ga Rayuwar su da ayyukan noma.

Jaridar Solacebase ta bada labarin cewa a ranar Alhamis din da ta gabata, Dam din tiga ya mamaye gabar kogin zuwa filayen gonakin noma da gidajen jama’a da dama a yankin sakamakon kwararar ruwa da aketa samu akai akai a kwanakin nan.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin Dan Majalisar Fatihu Yusif Bichi ya fitar, Rurum ya yi wannan kiran ne bayan da yakai wata ziyara yankin sakamakon ambaliya da ruwan ya shafi dubban jama’a tareda awon gaba da gonaki da lalacewar hanyoyi dakuma tilastawa kauyukan da ke kewaye ranta a na kare dan gudun tsira.

Sanarwar ta ce a yayin ziyarar, tsohon kakakin majalisar dokokin Kano ya ce bisa ga bayanan da ya samu daga wadanda abin ya shafa, sun yi zargin cewa hukumar raya kogunan Hadejia da Jama’are ta yi kaca-kaca da madatsar ruwan da aka yi a yankin, wanda daga baya ke cigaba da barazana ga al’umma.

“Sakamakon kwararar dam din na tiga ya haifar da ambaliya kuma dubban mazauna yankunan tuni sukai gudun hijira,” in ji Rurum.

Da yake zantawa da Solacebase Dan Majalisar Alhassan Rurum, ya ce ya tattauna da manajan daraktan hukumar kula da kogunan Hadejia da Jama’are domin tsara hanyoyin da za a hana afkuwar lamarin anan gaba.

Ya yi alkawarin gabatar da batun a zauren majalisar wakilai domin gudanar da bincike tare da dakile barazanar da ka iya tasowa nan gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here