Hukumar kula da Gidajen gyaran hali ta Ƙasa NCoS, ta tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kai hari a gidan gyaran hali na Kuje, da ke Abuja babbab birnin tarayyar Najeriya, ranar Talata da daddare.
Hakan na dauke cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Umar Abubakar ya fitar.
Sanarwar ta ce “wasu ‘yan bindiga da ba a tantance ko su wane ba sun kai hari gidan gyaran hali na Kuje, da ke yankin babban birnin tarayyar Najeriya.”
“jami’an hukumar tare da taimakon sauran jami’an tsaro sun mayar da martani kan maharan, kuma yanzu haka an mayar da doka da oda a gidan.”










































