2023: Kwankwaso ya sanya ranar da zai Kaddamar da takarar sa

RMK RMK
RMK RMK

Tsohon gwamnan jihar Kano, Engineer Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro a kasar nan, kan su kara kaimi wajen shawo kan matsalolin tsaron da suka yi kamari a kasar nan.

Kwankwaso ya yi wannan kira ne a wani taron manema labarai daya kira ranar Juma’a a Abuja.

Kwankwaso yace akwai bukatar hukumomi su ci gaba da kokarin dakile yaduwar ayyukan ta’addanci a kasar nan.

Dan takarar neman shugabancin Najeriyar, a karkashin jam’iyar NNPP, ya koka matuka da irin mawuyacin halin da kasar ke ciki ta fuskar tsaro, yana mai cewa akwai bukatar a kawo karshen lamarin da gaggawa.

“ Kasancewata tsohon ministan tsaro a kasar nan amma ban taba tsammanin cewa al’amuran tsaro zasu dugule kamar yadda suke a yanzu ba, a rayuwa ta” inji shi.

“Akwai bukatar shugabanni su rinka karawa dakarun sojojin kasar nan kwarin gwiwa ta hanyar basu horo akan sababbin dabarun yaki na zamani tare da wadatasu da sababbin makaman yaki na zamani da zasu kawo karshen yaduwar ayyukan ta’addanci a kasar nan” a cewar sa.

“Nayi imanin cewa lalle akwai bukatar gwamnati ta yi abin daya dace, domin halin da ake ciki ta fuskar tsaro yana sake saka takaici a zukatan mu”

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kara da cewa “tsaro na cikin jerin abubuwan da yakamata a ingantashi, domin a baiwa jama’ar kasa damar gudanar da ayyukan su na yau da kullum cikin walwala da aminci”.

“Haka kuma zabe mai zuwa a shekara ta 2023 zai kasance a tsakanin mutanen da suke so a ci gaba da tafiya a halin da ake ciki na dagulewar tsaro, ko kuma a yi kokarin kawo sauyi domin a ceto Najeriya daga mawuyacin halin da take ciki” inji Kankwaso

Madugun na Kwankwasiya, yace bayan dana tuntubi, duk wanda ya kamata na tuntuba, zan kaddamar da muradina na neman shugabancin kasar nan a mako mai zuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here