Wasu da ake zargi ’yan daba ne sun kai hari kan ayarin motocin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, tare hanyar shiga jihar Benue.
Mai daukar hoton yakin neman zaben Obi, Esther Umoh, ce ta bayyana haka a ranar Talata a wani sako da ta wallafa a shafin X tare da bidiyon lamarin.
Umoh ta ce ayarin motocin sun isa jihar ke nan lokacin da ‘yan dabar da ake zargin suka tare titin Boko kusa da sansanin sojin sama, inda ake zargin sun yi hakan ne domin su hana Obi shiga jihar.
“Mun riga mun isa jihar Benue, inda wasu da ake zargi ’yan daba ne da aka dauki nauyinsu suka tare titin Boko kusa da sansanin sojin sama, suna kokarin hana Peter Obi shiga jihar,” in ji ta.












































