Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sa ranar 19 ga Satumba domin gudanar da zaben cike gurabi 5 a jihohin Najeriya 4 da suka hada da Gombe, Kano, Bauchi da Delta.
Sakataren Yada Labara Shugaban INEC, Mr. Tunde Oketola, ne ya bayyana hakan a cikin hirar da ya yi da kamfanin dillacin labarai na kasa (NAN) a ranar Talata a Abuja.
Oketola ya ce zaben cike gurabin ya kunshi na dan majalisar tarayya 1 da majalisun dokoki jihohi 4.
A cewar Oketola, za a gudanar da zaben cike gurabin a Mazabar Gombe, Kwami da Funakaye a Jihar Gombe.
Na mazabun jihohi kuma sun hada da: Mazabar Disina da Sakwa a Jihar Bauchi, Udu a Jihar Delta da Dawakin Kudu a Jihar Kano
(NAN)













































