Jarumin wakar Afrobeats, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya bayyana yadda Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da dan kasuwa Aliko Dangote suka yi kokarin shawo kansa ya goge rubutunsa a shafin sada zumunta yayin zaben gwamnan Jihar Osun.
Davido ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da News Central TV a ranar Talata, yayin da yake bayani kan matsin lamba da ya fuskanta yayin da yake sanya ido kan zaben yana wallafa bayanai a X, wanda a da ake kira Twitter.
Mawakin ya zargi ‘yan siyasa da fitar da kudi mai yawa domin yin tasiri a zaben, yana mai cewa an kawo sama da Naira biliyan 110 cikin jihar.
“Yau na tabbatar. Sun kashe Naira biliyan 110. Ina zuwa wani wuri da muke da wanda yake ciki yana bamu labari… Idan kun ga kudin da wadannan mutane suka kawo. Da sun yi nasara a wannan zaben, Najeriya ta kare. Domin tsarin zabe zai zama tashin hankali da kudi,” in ji shi.
Davido ya ce tawagarsa ba su raba kudi ga masu jefa kuri’a a ranar zabe ba, sai dai sun dogara ne kan fadakar da masu jefa kuri’a don su goyi bayansu.
“Ba mu kashe ko sisin a ranar zabe ba. Abin da kawai mu ka yi fata shi ne wadannan mutane su karbi kudin su kuma zabe mu,” in ji shi.
Ya kara da cewa wasu mazauna jihar sun fuskanci matsalar mutanen da ake zargin suna kokarin lalata zaben.
“Ya kai wani mataki har sai da mutanen Osun suka yi wa wadanda ke kokarin kwace akwatin zabe duka. Jama’a sun gaji,” in ji shi.
Mawakin ya kuma bayyana cewa ya sami kira daga manyan mutane yayin da ake tattara kuri’u, inda suka roke shi ya goge rubutun sa.
“Na ji Shugaban Majalisar Dattawa yana kokarin kiran cibiyar tattara sakamako… Suna kiran na goge. Na ce a’a. Ku duka kun taro don adawa da Kawuna… Ba zan goge komai ba. Kawo Aliko ma ya kira ni. Na ce, ‘Kawu, ba zan goge ba har sai INEC ta sanar,’” in ji shi.
Davido ya ce nasar kawonsa, Gwamna Ademola Adeleke, ta nuna cewa goyon bayan jama’a zai iya kayar da tasirin kudi da siyasa.
“Kawona ya zama misali ga sauran jami’an gwamnati da gwamnoni. Idan ka tsaya tare da jama’a, jama’a za su tsaya tare da kai,” in ji shi.
Shigewar Davido cikin siyasar Osun na da alaka da tarihin siyasar danginsa a jihar. Marigayi kawonsa, Sanata Isiaka Adeleke, wanda aka fi sani da Serubawon, shi ne gwamna na farko na farar hula na Jihar Osun a 1992, yayin da dan uwansa, Ademola Adeleke, shi ne ke gwamna na yanzu.













































