Gwamnatin Osun ta garzaya kotu don kalubalantar kulle asusunta da EFCC ta yi

EFCC Osun

Gwamnatin Jihar Osun ta fara shirin daukar matakin shari’a kan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta (EFCC), sakamakon kulle asusun bankin ta.

Gwamnatin ta kuma bayyana matakin EFCC din a matsayin wanda yake ba bisa doka ba kuma zai iya kawo cikas ga ayyukan gwamnati.

Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Oluwole Jimi-Bada, ne ya sanar da hakan a ranar Laraba.

A cewar kwamishinan, Gwamna Adeleke ya ba shi umarni ya shigar da kara a gaban Babbar Kotun Tarayya domin kalubalantar matakin hukumar yaki da cin hanci.

Jimi-Bada ya bayyana cewa “gwamnatin jihar ta samu bayanin cewa EFCC ta baiwa First Bank umarnin Post No Debit, inda ake adana yawancin asusun gwamnati, wanda hakan ya hana yin kowace mu’amala a asusun”.

“ko da yake EFCC na da ikon binciken mu’amalolin kudi, amma ba ta da ikon kulle asusun gwamnatin jihar ba tare da samun umarnin kotu ba”.

“Na karbi umarnin gwamna na garzaya Babbar Kotun Tarayya domin kalubalantar wannan mataki. EFCC na iya binciken asusun, amma ba za ta iya kulle asusun ba tare da umarnin kotu ba,” in ji shi.

Ya ce hana amfani da asusun na iya shafar ayyukan gudanar da gwamnati na yau da kullum da kuma bayar da ayyukan ga jama’a a fadin jihar.

“Wannan mataki zai shafi gudanar da gwamnati amma za mu kalubalanci shi kuma mu tabbatar hukumar ta yi aiki bisa iyakokin doka,” in ji shi.

A nasa bangaren, Kwamishinan Kudi, Sola Ogungbile, ya zargi cewa jami’an ‘yan sanda sun kai ziyara babbar reshen First Bank dake Osogbo suka kama wasu daga cikin ma’aikatan bankin yayin da lamarin ke faruwa.

Ogungbile ya kuma musanta jita-jitar da ke cewa ana amfani da kudaden jihar wajen daukar nauyin yakin sake zaben Gwamna Adeleke, yana mai jaddada cewa ba a karkatar da kudaden jama’a zuwa harkokin siyasa ba.

Ya roki ga hukumar yaki da cin hanci da ta yi la’akari da yadda hana amfani da asusun zai shafi gudanar da mulki da walwalar mazauna jihar da ke dogaro da ayyukan gwamnati.

A wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Wayar da Kai, Kolapo Alimi, ya fitar a baya, gwamnan ya bayyana matakin a matsayin wanda ba shi da hujja a doka, yana mai zargin cewa an yi shi ne domin kawo cikas ga ayyukan gwamnati gabanin zaben gwamna na ranar 15 ga Agusta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here