Gwamna Yusuf ya sanya hannu kan dokar zartarwa don yaki da shan miyagun kwayoyi da daba

WhatsApp Image 2025 04 25 at 08.51.59 750x430

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Yusuf, a ranar Laraba ya sanya hannu kan Dokar Zartarwa domin yaki da safar miyagun kwayoyi, shaue-shaye da ayyukan daba a jihar. Wannan na daga cikin kokarin magance karuwar rashin tsaro da laifuka a jihar.

Hakazalika, Gwamna Yusuf ya kaddamar da wani kwamitin hadin gwiwa na yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi domin tabbatar da bin dokar da kuma daidaita matakan da jihar ke dauka kan wannan barazana da ke kara yaduwa.

Yayin da yake jawabi a wurin taron sanya hannun a Kano, Yusuf ya ce shan miyagun kwayoyi na daga cikin barazanar da ke fuskantar matasan jihar, inda yace hakan na haifar da laifukan tashin hankali, ruguza iyalai, raunana tattalin arziki kuma yana lalata zaman lafiyar al’umma.

Ya ce Dokar Zartarwar da ta fara aiki nan take ta hana sayarwa da safar miyagun kwayoyi tare da rarraba magungunan da basu da rajista ba tare da takardar likita mai iganci ba.

Gwamnan ya kara da cewa za a takaita zirga-zirga daga karfe 6 na yamma zuwa 10 na safe a wuraren da aka gano sun shahara da shan miyagun kwayoyi a fadin jihar. A lokaci guda kuma an ba hukumomin tsaro izinin tsayawa, bincike, kama da gurfanar da duk wanda ake zargi.

Yusuf ya kuma bayyana cewa gwamnati za ta kwace Takardun Mallakar Kasa na duk wani gida ko wuri da ake amfani da shi wajen sayarwa ko safarar miyagun kwayoyi.

A cewarsa, Dokar Zartarwa kan ayyukan daba tana samar da ingantaccen tsarin shari’a domin tarwatsa kungiyoyin masu laifi, dakile tashe-tashen hankula na siyasa da kuma karfafa kokarin hukumomin tsaro na tabbatar da doka da oda.

Ya ce an ba kwamitin aikin ganowa tare da tarwatsa matattarar kungiyoyin ‘yan daba da wuraren shaye-shayen kwayoyi ba bisa ka’ida ba, gami da kama da gurfanar da shugabannin kungiyoyin, mambobi, masu daukar nauyi da masu ba da kudi da ke da hannu a laifukan da suka shafi kwayoyi.

Gwamnan ya ce wannan mataki yana da goyon bayan sashi na 97A na Dokar Shari’ar Kano da kuma Sashe na 89 na shekarar 1991.

Ya yi alkawarin samar da isasshen kudi, motoci, ofis, kayan aiki da tallafin tsaro ga kwamitin, tare da tabbatar musu da ‘yancin gudanar da aiki ba tare da tsangwama ba.

Yusuf ya kuma ce jihar ta kafa cibiyoyin gyara dabi’u daban-daban na maza da mata da suka kamu da shan miyagun kwayoyi, kuma za su ci gaba da karfafa shirye-shiryen gyara da mayar da su cikin al’umma.

Shugaban kwamitin, Barrista Muhuyi Magaji ya yi alkawarin gudanar da aikin kwamitin cikin gaskiya da sana’a.

Ya ce mambobin za su yi aiki tare da hukumomin tsaro, sarakuna, malamai, kungiyoyin farar hula da na al’umma domin yakar shan miyagun kwayoyi da dawo da zaman lafiya a fadin jihar.

Kwamiin ya kunshi wakilai daga hukumomin tsaro ciki har da ‘Yan Sanda, SSS, NDLEA, Hukumar Kwastam, Hukumar Shige da Fice da NSCDC. Har ila yau akwai wakilai daga kungiyoyin farar hula, masarautu, kungiyoyin addini da ‘yan kasuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here