’Yan bindiga sun yi garkuwa da ’yar uwar tsohon Ministan Lantarki kuma dan takarar gwamnan APC na 2027 a Jihar Oyo, Bayo Adelabu, tare da ’ya’yanta tagwaye maza a Ibadan, babban birnin jihar.
Wani shaidar gani da ido ya ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba a yankin Challenge da ke Karamar Hukumar Ibadan South West ta jihar.
Da yake tabbatar da lamarin a wata sanarwa, daya daga cikin mataimakan yada labarai ga Adelabu, Femi Awogboro, ya ce, “Iyalin Adebayo Adelabu, tsohon Ministan Lantarki kuma dan takar gwamna navjam’iyyar APC a Jihar Oyo, sun tabbatar da lamarin garkuwa da kanwar Olaide Busayo Adegoke John-Paul, tare da ’ya’yanta tagwaye maza, Peter da Paul, da safiyar ranar Laraba, 3 ga Yuni 2026.
“An ruwaito cewa ’yan bindigar dake dauke da makamai sun yi garkuwa da Mrs. Olaide Busayo Adegoke John-Paul mai shekara 43 da misalin jarfe 7:30 na safe yayin da take kan hanyarta ta kai ’ya’yanta makaranta a Ibadan. Masu garkuwa da mutanen sun kuma yi garkuwa da ’ya’yanta tagwaye maza masu shekara 12 da ke tare da ita a lokacin da lamarin ya faru.
Idan za a iya tunawa, sama da malamai da dalibai 40 aka yi garkuwa da su a ranar Juma’a, 15 ga Mayu 2026, yayin wani hari da aka kai a Ahoro-Esiele dake Karamar Hukumar Oriire ta jihar.












































