Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya koma Abuja a ranar Lahadi bayan wakiltar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a Taro na 39 na yau da kullum na Majalisar Shugabannin Ƙasashe da Gwamnatocin Tarayyar Afirka (AU).
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa taron ya gudana tsakanin ranar Asabar da Lahadi, mai taken, “Tabbatar da dorewar samar da ruwa da ingantattun tsarin tsaftar muhalli domin cimma manufofin Ajandar 2063.”
Taron ya mayar da hankali kan ƙarfafa alkawuran nahiyar wajen kula da ruwa mai dorewa, inganta tsarin tsaftar muhalli, da kuma burin ci gaban da ke kunshe cikin tsarin Ajandar 2063 na AU.
Baya ga zaman shugabannin ƙasashe, Shettima ya halarci manyan tarurrukan gefe da kuma ganawa da shugabannin siyasa da na kasuwanci domin ƙarfafa hulɗar diflomasiyya, tattalin arziki da dabarun haɗin gwiwa tsakanin Nijeriya da sauran ƙasashen nahiyar.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya samu goyon bayan Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, wanda ya buƙaci Najeriya ta jagoranci yunƙurin Afirka na samar da sabon tsarin duniya.
Shettima ya kuma yi kira da a sauya akalar nahiyar zuwa cikakken ikon kula da tsaron lafiyar al’umma, domin kaucewa dogaro da tallafin ƙasashen waje, tare da gina tsarin kiwon lafiya mai cin gashin kansa a cikin gida.
(NAN)













































