Gabanin shirin sauya sheƙar gwamnan Kano Abba, Ganduje ya dawo daga Dubai

Ganduje arrives 720x430

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya dawo Najeriya bayan shafe makonni yana hutu a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa.

Dawowar Ganduje na da alaƙa da kammala shirye-shiryen sauya sheƙar gwamnan Kano tilo na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC.

A wata sanarwa da shugaban ma’aikatansa, Muhammad Garba, ya fitar, Ganduje ya sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, kafin ya wuce Abuja domin ci gaba da wasu muhimman ayyuka na siyasa.

Sanarwar ta bayyana cewa bayan dawowarsa, tsohon shugaban APC na ƙasa zai fara jerin shawarwari da tarurrukan masu ruwa da tsaki kan abubuwan siyasa da ke gudana a Jihar Kano.

Wadannan tattaunawa za su mayar da hankali ne kan duba yanayin siyasar jihar da kuma tuntubar shugabannin jam’iyya da manyan jiga-jigan siyasa domin samun fahimta mai zurfi.

Haka kuma, ana sa ran Ganduje zai shiga aikin sabun rajistar mambobin APC da ake yi a fadin ƙasa, wanda shi ne ya assasa tsarin a lokacin da yake shugabancin jam’iyyar domin inganta bayanan mambobi da tsare-tsaren cikin gida.

Sanarwar ta kara da cewa Ganduje na da kudirin karfafa ginshikan jam’iyyar APC da kuma inganta tattaunawa mai bude kofa domin karfafa dimokuradiyya a cikin jam’iyyar, musamman a Jihar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here