A shirye muke mu karɓi Gwamna. Kano a Jam’iyyar APC – Shugaba

Abdullahi Abbas APC 1

Jam’iyyar APC a jihar Kano ta sake jaddada cewa tana cikin cikakken shiri na karɓar Gwamna Abba Kabir Yusuf cikin jam’iyyar, gabanin shirin sauya sheƙarsa daga jam’iyyar NNPP.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya aikawa kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN a Kano.

Abbas ya bayyana cewa wannan mataki yana tafiya ne bisa turbar haɗin kai, sasanci da kuma la’akari da muradun al’ummar jihar Kano gaba ɗaya.

Abdullahi Abbas ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a madadin jagoran jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Ganduje, inda ya jaddada cewa kiran da ake yi wa Gwamna Yusuf ya shigo APC yana da nufin gina Kano mai haɗin kai da ci gaba.

Karanta: A Gaggauce: NNPP ta kori shugaban jam’iyyar na Kano, Dungurawa makonni biyu bayan sake zaɓensa

Ya ƙara da cewa jam’iyyar APC a shirye take ta karɓi Gwamna Yusuf hannu bibbiyu domin a haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen bunƙasa ci gaban jihar Kano.

A cewarsa, da zarar Gwamna Yusuf ya kammala sauya sheƙa, shi da sauran jiga-jigan NNPP za su shiga APC ne ƙarƙashin jagorancin Ganduje, cikin yanayi na mutunta juna da ɗaukar alhakin ciyar da jam’iyya da jihar gaba tare.

Sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da rade-radin sauya sheƙar gwamnan Kano zuwa jam’iyyar APC.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here