Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya isa Legas a ranar Juma’a domin ziyarar aiki, a daidai lokacin da Najeriya ke shirin bikin cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Mista Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Juma’a a Abuja.
Tinubu ya wuce Legas ne bayan halartar bikin nadin sabon Olubadan na Ibadanland, Oba Rashidi Ladoja, a Jihar Oyo.
A yayin da yake Legas, ana sa ran shugaban ƙasar zai gana da manyan shugabannin sashe masu zaman kansu tare da manyan jami’an gwamnati.
Sanarwar ta ƙara da cewa shugaban ƙasar zai tafi Jihar Imo a ranar Talata domin kaddamar da muhimman ayyuka da Gwamna Hope Uzodimma ya aiwatar.
Haka kuma, a cikin shirye-shiryen bikin ranar ‘yancin kai, shugaban ƙasar zai kaddamar da filin wasan kwaikwayo da al’adu na ƙasa da aka sake fasalta a Legas, wanda yanzu aka sake masa suna Wole Soyinka.
NAN












































