An yi jana’izar tsohon Shugaban Rundunar Sojoji, Mohammed Inuwa Wushishi

Mohammed Inuwa Wushishi
Mohammed Inuwa Wushishi

An yi jana’izar tsohon Shugaban Rundunar Sojoji, Mohammed Inuwa Wushishi Mai Ritaya a garin Kaduna.

An gudanar da sallar jana’izar ne a Masallacin Sultan Bello dake Kaduna, inda babban limamin masallacin Sheikh Ahmad Gumi ya jagoranci sallar.

Jana’izar ta samu halartar tsohon shugaban kasa Abdussalam Abubakar, da Ministan tsaro Bashir Magashi, da kuma babban hafsan sojojin Nigeria laftanar Janar Farouk Yahaya, da sauran manyan mutane.

An haifi marigayi Mohammed Inuwa Wushishi a garin Wushishi dake jihar Niger a shekarar 1940, inda ya shiga aikin soja a shekarar 1961. Ya kasance shugaban sojojin Nigeria a zamanin mulkin shugaban kasa Shehu Shagari daga watan Octoba na shekarar 1981 zuwa Octoba na shekarar 1983.

Mohammed Inuwa Wushishi ya rasu ne a ranar asabar 5 ga watan Disamba a birnin London dake kasar Ingila.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here