Gwamnatin tarayya ta ce, kamfanin da ya mallaki dandalin sada zumunta na Twitter, ya amince da dukkan sharuɗɗan da aka gindaya game da ayyukansa a Najeriya.
Ƙaramin Ministan kwadago da aiki Barista Festus Keyamo ne ya sanar da hakan ga Gidan Talabijin na Channels a wani shirin siyasa.
Ministan wanda kuma mamba ne a kwamitin da aka kafa domin duba ayyukan dandalin tun bayan da aka dakatar da shi a ranar 4 ga watan Yunin da ya gabata, ya ce kwamitin ya samu ci gaba sosai a ayyukan da ya gudanar.
Idan dai za a iya tunawa, Ministan yaɗa labarai, al’adu da yawon buɗe ido, Lai Mohammed, ne ya sanar da dakatarwar.
Lai ya ce, “Dalilin da ya sa shugaban ƙasa ya ɗauki wannan mataki shi ne don sake dai-daita dangantakarmu da Twitter ba wai don korar su daga kasarmu ba.”
Ya ci gaba da cewa: “Wannan sake fasalin, mun fara shi kuma shugaban ƙasa ya ƙara da ni a cikin kwamitin.
“Mun kuma kafa wani kwamitin fasaha da zai yi mu’amala da Twitter tare da samar da wasu sharudda da yawa domin su cika mana mu ɗage dakatarwar.
“Twitter ne ya tuntuɓi gwamnatin tarayya inda suka ce suna son sanin abin da za su iya yi don dai-daita dangantakar da ke tsakaninta da gwamnatin tarayya.










































