Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umarci jami’an hukumar tsaro na farin kaya (DSS) da su bar ofishin hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) da ke Ikoyi, Legas cikin gaggawa. A labarin da Legit.ng ta wallafa a baya, mun kawo muku cewa jami’an hukumar DSS sun yi wa ofishin hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ƙawanya da safiyar ranar Talata.
Bayan haka, jami’an na farin kaya, a cikin wasu motoci guda biyu masu ɗauke da makamai, sun tare babbar kofar shiga ofishin.
Mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, da aka tuntuɓe shi, ya bayyana faruwar lamarin a matsayin wani baƙon abu. Ya bayyana cewa hukumomin biyu sun zauna tare a cikin ginin na sama da shekaru 20 ba tare da wata ɓaraka ba.













































