MB Shehu na NNPP ya Doke Dan majalisar APC Mai ci a Kujerar Fagge

NNPP
NNPP

Dan majalisar wakilai mai ci a karamar hukumar fagge, Aminu Sulaiman Goro na jam’iyyar APC wanda ke wa’adi na 3 a majalisar wakilai ta kasa ya sha kashi hannun MB Shehu na jam’iyyar NNPP.

Jami’in bayyana zaben, Farfesa Ibrahim Tajo Suraj, a lokacin da yake bayyana sakamakon zaben, ya ce MB Shehu ya samu kuri’u 19, 024 na jimillar kuri’un da aka kada, sai dan takarar jam’iyyar Labour, Shuaibu Abubakar wanda ya samu kuri’u 12,789.

Hakazalika, Aminu Sulaiman Goro na APC ya zo na uku da kuri’u 8,669.

“Barrister MB. Shehu na jam’iyyar NNPP, bayan ya cika sharuddan doka kuma ya samu mafi yawan kuri’u an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben,” in ji jami’in zaben.

Tun da farko dai jam’iyyar NNPP ce ke kan gaba da kuri’u 609 a zaben cike gurbin, yayin da APC ta zo ta biyu da kuri’u 268, sai LP da kuri’u 60.

Sai dai a lokacin da aka tattara sakamakon zaben da ya gabata a ranar 25 ga watan Fabrairu, jam’iyyar NNPP ta zo ta daya sai LP da APC a matsayi na biyu da na uku.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here