Zargin batanci: Akpabio da Yahaya Bello ba su da mutuncin da za su kare – Natasha ta faɗa a gaban kotu

Natasha Akpoti Uduaghan 750x430

Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta shaidawa babbar kotun tarayya dake Abuja cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ba su da kyakkyawan suna da za a kare, tana mai cewa kalamanta da suka danganta su da yunkurin kisan gilla a kanta ba batanci ba ne.

Natasha ta bada wannan hujja ne a cikin wata ƙarar da ta yi watsi da ita wadda ta shigar, kan zargin batanci da cin zarafin mutane ta hanyar amfani da internet da gwamnatin tarayya ta kai a gaban kotu.

A cikin ƙarar da aka shigar ranar 18 ga Satumba, mai lamba CR/195/25, ta hanyar lauyanta Michael Numa, ta bayyana cewa Akpabio da Bello sun taɓa yin amfani da mukamansu ba bisa doka ba lokacin da suke gwamnoni, inda aka zargi Akpabio da haifar da tashin hankali a lokacin mulkinsa a Akwa Ibom, da kuma Bello da almundahanar kuɗin jihar Kogi.

Ta ce waɗannan zarge-zargen sun fi tsanani fiye da abin da ake tuhumarta da shi na batanci, don haka tuhumar gwamnati ba ta da tushe.

A cikin rantsuwar shaidar da ta gabatar mai shafi 17, Natasha ta ce karar batanci da cin zarafi ta hanyar internet ba don maslahar jama’a aka shigar ba, sai dai don kare muradun Akpabio da Bello.

Ta kuma bayyana cewa maganganunta sun shafi rayuwarta kai tsaye, ba aikin ofishinsu ba.

Sanatar ta ƙara zargin cewa ‘yan sanda ba su gudanar da cikakken bincike kafin gwamnatin tarayya ta ɗauki matakin gurfanar da ita a gaban kotu ba, tana mai cewa shari’ar siyasa ce da ke nuna amfani da ofishin babban lauyan ƙasa ta hanyar da ba ta dace ba.

Gwamnatin tarayya dai ta shigar da ƙarar batanci guda biyu a kanta, ta farko mai lamba CR/297/25, da aka shigar a ranar 16 ga Mayu, bisa dokar Penal Code, inda ake tuhumarta da yin maganganu da ka iya ɓata suna.

Wannan na da alaƙa da hirar da ta yi a tashar Channels Television a ranar 3 ga Afrilu, inda ta bayyana cewa rayuwarta na cikin haɗari bayan an janye mata jami’an tsaro, tare da zargin Akpabio da Bello da hannu a lamarin.

Ƙarar ta biyu mai lamba CR/195/25 kuwa, ta ƙunshi ƙarin bayanai kan waɗannan maganganu da ta sake maimaitawa a lokacin bikin dawowarta gida a yankinta a ranar 1 ga Afrilu, inda ta ce mutanen biyu na ƙoƙarin kashe ta saboda ta ƙi amincewa da matsin lambar siyasa da kuma yunƙurin tsige ta daga majalisa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here